<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>191</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Dā, na zauna cikin zunubi,
 Ba na kula da Ubangiji,
 Ko mutuwa wadda shi ya yi
 Kan giciye.

[V2]
 KORUS
 Jinƙan Yesu, ba misalinsa,
 Ya yi mini aikin gafara.
 Kayan laifina ya ɗauka kuwa
 Kan giciye.

[V3]
 2) Na ji zancen ladan zunubi.
 Tsoron mutuwa ya kama ni.
 Sai na roƙi jinƙan Mai Ceto
 Kan giciye.
 Korus

[V4]
 3) Na yi murna marar iyaka
 Tun da Yesu ya yi cetona.
 Ina rera waƙar yabonsa,
 Ba fasawa.

[V5]
 4) Nufina in kawo daraja
 Wurin Yesu Ubangijina,
 Sa'an nan in dubi fuskarsa
 Har abada.</lyrics>
<title>Dā, Na Zauna Cikin Zunubi LW191</title>
</song>